Nijar da Jamhuriyar Benin sun amince da yin aiki a tare don yaƙi da ta’addanci da ke addabar ƙasashen biyu na Yammacin Afirka, yayin da a hannu ɗaya suka kafa wani kwamitin da zai bayar da shawarwari cikin kwanaki 15 a game da yadda za a sake buɗe iyakokin ƙasashen da ke rufe yau kusan shekaru uku.