Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta dakatar da shirin yin afuwa ko kuma sauya ɗabi’un tubabbun ƴan ta’adda a wani yunƙuri na dawo da su cikin al’umma, wanda ta ce ba ya taimakawa ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen yaƙi da ta’addancin da ya yi mata katutu.