A Najeriya, ƙungiyar G –100 ta gamayyar wasu fitattun ƴan ƙasar kimanin 100 ta jagorancin wani sabon yunkurin ganin lallai sai jam’iyyun adawa sun yi haɗin guiwa domin fitar da ɗantakara ɗaya tilo da zai fafata da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara mai zuwa.