A Najeriya, Gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyar Accord Ademola Deleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar da ƙuri’u sama da dubu 511, yayin da ɗan takarar jam’iya APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji yazo na biyu da ƙuri’u dubu 444,815.